Skip to content

Latest commit

 

History

History
314 lines (157 loc) · 18.8 KB

hausa.md

File metadata and controls

314 lines (157 loc) · 18.8 KB

BBC News Hausa

Hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta sake yi kan rikicin masarautar Kano

Jummaʼa 14 Maris, 2025 da 5:44:40 Yamma

A ranar Juma'ar nan ne kotun ɗaukaka ƙara a Abuja ta jingine hukuncin da ta yi a watan a ranar 10 ga watan Janairun 2025 kan rikicin masarautar Kano, har zuwa lokacin da kotun ƙoli za ta yanke hukuncin ƙarshe dangane da rikicin.

Gwamnatin Najeriya ta musanta kashe Kiristoci da gangan a hare-haren 'yan fashin daji

__

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 14/03/2025

Tungar yaƙin Taliban a Afghanistan na farfaɗowa bayan shekara 20

Jummaʼa 14 Maris, 2025 da 6:29:07 Yamma

Yayin wani balaguro da ba a saba yi ba zuwa Sangin, BBC ta ga yadda garin ke farfaɗowa bayan yaƙin shekara 20 tsakanin Taliban da dakarun ƙasashen Yamma.

Mece ce makomar Gwamnan Rivers, Simi Fubara a siyasa?

Jummaʼa 14 Maris, 2025 da 3:38:41 Safiya

Ko a ranar Talata, Nyesom Wike, ya ce babu abin da zai faru idan majalisar dokokin jihar ƙarƙashin jagorancin Amaewhule ɗin ta tsige gwamnan jihar, Siminalayi Fubara.

Girke-girken Ramadan: Yadda ake sarrafa farfesun kan rago da funkaso na alkama

Jummaʼa 14 Maris, 2025 da 6:25:20 Yamma

A filinmu na girke-girken Ramadan na yau, Zakeeyah Idris wadda aka fi sani da Zakeeyahs Kitchen za ta nuna muku yadda ake sarrafa farfesun kan rago tare da funkaso na alkama.

Putin ya gindaya sharuɗɗan tsagaita wuta a Ukraine

Jummaʼa 14 Maris, 2025 da 10:18:10 Safiya

A Fabarairun 2022 ne Rasha ta ƙaddamar da gagarumin hari inda ta mamaye Ukraine kuma a yanzu ta karɓe iko da kusan kashi 20 cikin 100 na yankunan Ukraine ɗin.

Ko tsufa na kawo makanta?

Jummaʼa 14 Maris, 2025 da 10:54:45 Safiya

Albarkacin makon yaƙi da cutar Glaucoma ta Duniya, Dakta Aisha Sheriff Kalambe ta faɗi yadda za ku iya gane ko kuna da Glaucoma mai janyo makanta.

Ko haƙar ƴan adawar Najeriya za ta cimma ruwa a zaɓen 2027?

Jummaʼa 14 Maris, 2025 da 3:44:42 Safiya

Shugabannin jam'iyyun adawa a Najeriya na ci gaba da kai wa juna ziyara, tare da bayyana aniyar hada hannaye don tunkarar babban zaben kasar na shekara ta 2027.

Wace ce Latifa al-Droubi - Uwargidan shugaban riƙo na Siriya?

Jummaʼa 14 Maris, 2025 da 3:40:46 Safiya

Sai dai ita sabuwar uwargidan shugaban ƙasa ba fitacciya ba ce. Duk da bayyana a taruka uku, har yanzu ba ta yi magana a bainar jama'a ba.

Chelsea ta amince da sayen Quenda kan fan miliyan 40

Jummaʼa 14 Maris, 2025 da 4:09:08 Yamma

Geovany Quenda na shirin komawa Stamford Bridge idan ya cika shekara 18 a 2026.

Kofin Carabao: Newscastle na neman lashe kofin farko cikin shekara 56

Jummaʼa 14 Maris, 2025 da 2:26:26 Yamma

Liverpool ce mai riƙe da kambun, inda ta doke Chelsea a kakar bara a ƙarƙashin jagorancin Jurgen Klopp kafin ya rabu da ƙungiyar a bara.

Salah ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Premier na wata karo bakwai

Jummaʼa 14 Maris, 2025 da 2:03:17 Yamma

Mohamed Salah ya lashe kyautar watan Fabrairu a matsayin ɗan wasan da ya fi hazaƙa, bayan da bajintar da ya yi a watan, a ƙoƙarin da ƙungiyarsa ke yi na lashe gasar Premier.

Real Madrid na son Fernandez daga Chelsea, Ƙungiyoyin Firimiya na rububin Gibbs-White

Jummaʼa 14 Maris, 2025 da 3:37:49 Safiya

Chelsea na iya amincewa Fernandez ya koma Madrid a wani ɓangare na musayarsa da ɗan wasan Faransa mai shekara 25, Aurelien Tchouameni.

Man United ta kai kwata fayinal a Europa bayan ruwan ƙwallaye a ragar Socieded

Alhamis 13 Maris, 2025 da 10:40:12 Yamma

Manchester United ta kai zagayen kwata fayinals a gasar zakarun Turai ta Europa League, bayan ta yi ruwan ƙwallaye 4-1 a ragar Real Socieded a wasa na biyu na zagayen 'yan 16.

Zan ci gaba da yaɗa manufofin jam'iyyar APC - Buhari

Alhamis 13 Maris, 2025 da 6:39:20 Yamma

Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce har yanzu shi ɗan jam'iyyar APC ne, kuma ya fi so a rinƙa alaƙanta shi da jam'iyyar wanda ta ba shi dama har wa'adi biyu.

Ƴanbindiga sun sace wanda ya lashe gasar karatun Al-ƙur’ani ta Najeriya

__

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 13/03/2025

Sai da Buhari ya amince sannan na bar APC zuwa SDP - El-Rufai

Alhamis 13 Maris, 2025 da 3:22:39 Safiya

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce bai bar jam'iyya mai mulki ta APC ba har sai da tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya amince da batun barinsa jam'iyyar APC da komawa jam'iyyar SDP.

Hanyoyi 5 na kare kai daga kamuwa da ciwon ƙoda

Alhamis 13 Maris, 2025 da 11:09:55 Safiya

Alkalumma sun nuna cikin mutum 10 a duniya daya daga cikinsu za a same shi da ciwon koda wanda ya nuna girman barazanar ciwon a duniya.

PDP ta yi taro don warware rikicinta na  cikin  gida

Alhamis 13 Maris, 2025 da 3:21:37 Safiya

Taron na zuwa ne bayan da kotun ƙoli ta yi watsi da buƙatar dakatar da aiwatar da hukuncin da wata babbar kotu ta yanke na tsige Sanata Samuel Anyanwu daga mukamin sakataren jam'iyyar na ƙasa, inda ta maye gurbinsa da Hon Sunday Udeh Okoye.

Girke-girken Ramadan: Yadda ake soyayyen dankali mai agada da kaza

Alhamis 13 Maris, 2025 da 6:24:35 Yamma

A filinmu na girke-girken Ramadan na yau, Chef Rahama Mato za ta nuna muku yadda ake yin 'loaded fries', wato soyayyen dankali wanda aka cakuda da plantain da kaza.

Cutuka biyar da ake ɗauka a lokacin zafi

Alhamis 13 Maris, 2025 da 3:21:55 Safiya

Galibin cututtuka sun fi haɓaka a lokacin zafi saboda yanayin tsaurin jiki da inda jiki ke tafiya.

Da gaske Amurka na shirin faɗawa karayar tattalin arziki?

Alhamis 13 Maris, 2025 da 3:22:20 Safiya

Tsare-tsaren Shugaban Amurka Trump na yin barazana ga tattalin arzikin ƙasar, inda ake fargabar zai faɗa cikin karaya.

Yadda za ku gane wanda ya kamu da cutar sanƙarau

Laraba 12 Maris, 2025 da 6:17:12 Yamma

Sanƙarau wata cuta da ke shafar fatar da ke kare ƙwaƙwalwa da kuma lakkar ɗan'adam - wato yaɗi guda uku da suka zagaye ƙwaƙwalwa da kuma lakka.

Sanata Natasha ta kai ƙarar Akpabio zuwa Majalisar Ɗinkin Duniya

Laraba 12 Maris, 2025 da 8:40:45 Safiya

Tun farko dai Sanata Natasha ta fito ta bayyana zarge-zargen ne bayan da a wani zaman majalisa aka ga yadda take ɗaga murya tana nuna fushinta game da yadda aka sauya mata wajen zamanta a majalisar ba tare da wani dalili ba, a cewarta.

Yadda abokina ya mutu a bola

Laraba 12 Maris, 2025 da 10:43:53 Safiya

Bolar Kiteezi da ke birnin Kampala na Uganda ta rufta ne a shekarar da ta gabata, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum 30 ciki har da abokin Sanya Kezia.

An hana gwamnan Rivers shiga majalisar dokokin jihar

__

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 12/03/2025

Yadda ƴanbindiga ke tarewa a yankin Bakori da Faskari

Laraba 12 Maris, 2025 da 3:22:27 Safiya

Rahotanni sun ce yanzu haka jama'ar garuruwa aƙalla shida na yankin ƙaramar hukumar Bakori suna can cikin tashin hankali mai tsanani.

Dabarun yin azumi a lokacin zafi

Laraba 12 Maris, 2025 da 3:23:05 Safiya

A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, Nimet ta ce za a samu ƙarin yanayin zafi na tsawon kwanaki uku zuwa huɗu, lamarin da zai iya jefa al'ummar jihohin cikin matsi.

Su wane ne masu aƙidar Alawi na Syria kuma me ya sa ake kai masu hari?

Laraba 12 Maris, 2025 da 2:37:22 Yamma

Mun duba dalilan da ya sa ake kai wa mabiya wannan ɗariƙa hari a baya-bayan nan da kuma aƙidojinsu.

Yadda China ke sauya fannin iliminta da ƙirƙirarriyar basira

Laraba 12 Maris, 2025 da 3:23:43 Safiya

China na fatan kashe sama da dala tiriliyan ɗaya domin gogayya da Amurka kan ƙirƙirarriyar basira.

Amurka ta miƙa tayin yarjejeniyar tsagaita yaƙin Rasha da Ukraine

__

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/03/2025

Me ya sa Saudiyya da Qatar suka fi jagorantar sasanci tsakanin ƙasashe?

Talata 11 Maris, 2025 da 4:36:17 Yamma

An zaɓi Saudiyya da Qatar domin shiga tsakani wajen samar da zaman lafiya a wasu muhimman tattaunawa a duniya.

Me Seyi Tinubu ke nema a ziyarce-ziyarcensa zuwa jihohin arewa?

Talata 11 Maris, 2025 da 3:59:26 Safiya

A karon farko wani ɗa ga shugaban ƙasa mai ci a Najeriya yake wani rangadi da ya kira na ƙulla zumunci da matasa irinsa da sauran al'ummar arewacin ƙasar.

Hikayata: Labarin Mugun Nama 9/3/25

Lahadi 9 Maris, 2025 da 2:28:35 Yamma

A filinmu na Hikayata a yau mun kawo maku 'Labarin Mugun Nama', wanda Fatima Isa da ke zaune a birnin Katsina ta rubuta, wanda kuma abokiyar aiki, Badriyya Tijjani Ƙalarawi ta karanta.

Amsoshin Takardunku 09/03/2025

Lahadi 9 Maris, 2025 da 2:11:34 Yamma

Shin waɗannna matakai ake bi kafin mutum ya zama Farfesan ilimi? Matakai nawa ne a tsarin aikin malamin Jami'a? Sannan menen bambancin Farfesa da Emiratus Farfesa?

Lafiya Zinariya: Abubuwan da ke janyo mace-macen mata masu juna biyu

Asabar 8 Maris, 2025 da 2:49:15 Yamma

Lafiya Zinariya: Abubuwan da ke janyo mace-macen mata masu juna biyu

Gane Mini Hanya: Kan Ranar Mata ta Duniya 08/03/2025

Asabar 8 Maris, 2025 da 2:46:04 Yamma

Kowacce shekara, tsawon sama da ƙarni guda, ana keɓe ranar 8 ga watan Maris a matsayin Ranar Mata ta Duniya.

Ra'ayi Riga: Kan hasashen saukar ruwan sama a Najeriya 07/03/2025

Asabar 8 Maris, 2025 da 1:50:49 Yamma

A shirinmu na wannan makon, mun duba tasiri da gargaɗin cewa ruwan sama zai yi saurin saka a wasu wuraren, sannan zai yi saurin ɗaukewa a wasu yankunan Najeriya, da kuma ko akwai wani shiri da manoma suke yi domin tunkarar wannan yanayin.

Mitocin da muke watsa shirye-shiryenmu

Jummaʼa 8 Disamba, 2023 da 6:50:55 Yamma

Sashen Hausa na BBC na watsa shirye-shirye guda huɗu a kowace rana, na tsawon minti talatin-talatin cikin harshen Hausa.